![Tsarin Fasahar Faifan CD (2)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/04/maadana-3.jpg)
Tsarin Fasahar Faifan CD (2)
Wannan ita ce kasida ta uku cikin jerin kasidun dake bayani kan ma’adanar bayanai, kuma ta biyu kan abin da ya shafi ma’adanar faifan CD, wato: “CD Plates”. A sha karatu lafiya.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
Wannan ita ce kasida ta uku cikin jerin kasidun dake bayani kan ma’adanar bayanai, kuma ta biyu kan abin da ya shafi ma’adanar faifan CD, wato: “CD Plates”. A sha karatu lafiya.
A cikin kashi na farko da muka gabatar mai taken: “Tarihin Ma’adanar Bayanan Sadarwa” watanni biyu da suka gabata, mai karatu ya samu mukaddima kan yadda dan Adam ya fara wayar da kansa sanadiyyar kalu-balen rayuwa da yake samu yau da gobe, cikin abinda ya shafi tsarin adanawa da kuma taskance bayanai; daga taskance su a kwakwalwansa, zuwa taskance su cikin ababen da ke muhallinsa.
A karshe dai, sabanin lokutan baya, a wannan zamani dan Adam ya nemo wasu hanyoyi masu sauki da ban mamaki da yake bi wajen taskance bayanai, da kuma nemo su cikin sauki ba tare da matsala ba. Dangane da haka muka ce zamu yi nazari na musamman kan ire-iren wadannan hanyoyi ko kayayyakin adanawa da kuma taskance bayanai da dan Adam ya kirkira, inda za mu fara da dubi kan tsari da kuma kimtsin da ke cikin Fasahar Faifan CD, watau Compact Disc Technology kenan a Turance. Amma kafin mu dulmiya kan tsarin Fasahar Faifan CD, zai dace mu yi waiwaye, abinda Malam Bahaushe ke kira “adon tafiya”.