Hira da Edward Snowden (3)
Ga kashi na uku na hirar Peter Taylor da Edward Snowden. A sha karatu lafiya.
Idan baka samu kasida ko maudu’in da kake nema ba…
A LURA: Dukkan kasidun dake wannan shafi suna da tsayi, domin kasidu ne da suka kunshi bincike na ilimi, ba wai labaru bane. Don haka, idan tsayinsu ya gundureka, kayi hakuri. Dabi’ar mahallin ne.
Ga kashi na uku na hirar Peter Taylor da Edward Snowden. A sha karatu lafiya.
Ga kashi na biyu na hirar Peter Taylor da Edward Snowden. A sha karatu lafiya.
Shahararren dan jarida Peter Taylor, wanda tsohon ma’aikacin BBC ne, ya samu daman hira da Edward Snowden, matashin nan dan kasar Amurka da ya hankado irin badakalar da ke kunshe shirin cibiyar tsaron kasar amurka na satar bayanan mutane da aiwatar da leken asiri cikin rayuwarsu, da sunan yaki da ta’addanci. Wannan kashi na daya ne.
A wannan makon ma ga mu dauke da karashen jawabin Edward Teller, wanda MALAM SADIK TUKUR GWARZO (sadiqtukurgwarzo@gmail.com) ya hakaito mana. A sha karatu lafiya.
Edward Teller masani ne a fannin kimiyyar sararin samaniya da kimiyyar sinadarai (Physics and Chemistry), kuma ya samar da ka’idojin bincike da kere-keren kimiyya a duniya da dama. Mutum ne mai wuyan sha’ani a lokacin rayuwarsa, kuma ya shahara wajen rajin kawo sauyin kere-kere a fannin kimiyyar sararin samaniya, inda ra’ayoyinsa suka bambanta matuka da ra’ayoyin abokan aikinsa a fannin ilimi. Duk da haka, ya yi hasashen yiwuwan faruwa ko rashin yiwuwan faruwar abubuwa da yawa a fannin kimiyya; wasu sun tabbata haka, kamar yadda mai karatu zai gani, wasu kuma basu tabbata ko ba, ana zaman jiransu. Wasu kuma, tarihi ya karyata shi a kansu. A yau za mu karantu wasu daga cikin hasashensa, wanda daya daga cikin masu karatu, mai kwazo da kokarin bincike, wato MALAM SADIK TUKUR GWARZO (sadiqtukurgwarzo@gmail.com) ya kawo mana. A sha karatu lafiya.
Wannan shi ne kashi na biyu na jawabin Steve Jobs. A sha karatu lafiya.
Steve Jobs, wato shugaban kamfanin Apple dake kasar Amurka dai Allah yai masa rasuwa. Saboda wannan munasaba muka ga dacewar kawo wani jawabi da yayi wa dalibai yayin yaye su a Jami’ar Standford dake kasar Amurka, a shekarar 2005. Wannan shi ne kashi na daya. A sha karatu lafiya.
Ga duk wanda ya saba bibiyar wannan shafi tun farkon farawa, ya san mukan yi zama lokaci zuwa lokaci, don yin nazari kan kasidun da muka gabatar a baya, da fa’idar da suka samar, da kura-kuran da aka nusar dani a kai in har akwai, da sakonnin masu karatu, sannan mu ga nan gaba ina muka dosa. Zuwa makon gobe in Allah Ya so za mu kawo sakonnin da kuka aiko ta waya ko ta Imel. Akwai sakonnin masu karatu da yawa a tare; wasu ta akwatin Imel ne, wasu kuma ta Facebook, wasu kuma ta wayar salula. Idan Allah Ya kaimu mako mai zuwa duk za mu zazzago su. Wannan ita ce marhala ta bakwai, tun farkon fara wanann shafi a shekarar 2006, cikin watan Nuwamba. Babu wani tazara ko ma’aunin watanni da muka sa don haddade kowace marhala. Mukanyi irin wannan zama ne kawai idan lokaci ya samu; iya gwargwadon hali.
Wadanda suka saba karanta wannan shafi tun farkon farawa sun san cewa a duk karshen zango, mukan zauna don yin waiwaye, abin da Malam Bahaushe ke kira “Adon tafiya.” A yanzu shekarun wannan shafi namu shida kenan da watanni shida cif-cif. Kuma wannan shi ne zama na shida da za mu yi, don yin bitar darussan da muka yi ta kwasa a baya. Ga wadanda basu san wannan tsari da shafin ke gudanuwa a kai ba, shafin Kimiyya da Kere-kere ya samo asali ne cikin watan Oktoba na shekarar 2006; farkon taken shafin shi ne: Kimiyya da Fasaha. Mun kuma yi waiwaye karo na daya, da na biyu, da na uku ne a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2008. Zama na karshe da muka yi, wanda shi ne waiwaye na hudu, ya zo ne cikin watan Satumba na shekarar 2008, daidai lokacin da shafin ya cika shekaru biyu kenan. Ga shi mun sake dawowa a yau don yin nazari kan kasidun baya, a karo na shida, kamar yadda masu karatu za su gani daga taken kasidar.
Wadanda suka saba karanta wannan shafi tun farkon farawa sun san cewa a duk karshen zango, mukan zauna don tattaunawa da juna, da kuma yin waiwaye, abin da Malam Bahaushe ke kira “Adon tafiya.” A yanzu shekarun wannan shafi namu biyar kenan da watanni shida cif-cif. Kuma wannan shi ne zama na biyar da za mu yi, don yin bitar darussan da muka yi ta kwasa a baya. Ga wadanda basu san wannan tsari da shafin ke gudanuwa a kai ba, shafin Kimiyya da Kere-kere ya samo asali ne cikin watan Oktoba na shekarar 2006; farkon taken shafin shi ne: Kimiyya da Fasaha. Mun kuma yi waiwaye karo na daya, da na biyu, da na uku ne a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2008. Zama na karshe da muka yi, wanda shi ne waiwaye na hudu, ya zo ne cikin watan Satumba na shekarar 2008, daidai lokacin da shafin ya cika shekaru biyu kenan. Ga shi mun sake dawowa a yau don yin nazari kan kasidun baya, a karo na biyar, kamar yadda masu karatu za su gani daga taken kasidar.
Na tabbata masu karatu sun lura da sauyin take da aka samu a wannan shafi, daga “Kimiyya da Fasaha” zuwa “Kimiyya da Kere-kere”. Hakan ba kuskure bane na mashin, lokaci ne yayi da ya kamata wannan sauyi ya samu. A takaice ma dai, har wasu cikin masu karatu sun bugo waya don nuna farin cikinsu da wannan canji da aka samu. Duk da haka mun ga dacewar gabatar da fadakarwa da kuma dalilan da suka haddasa hakan.
A yayin da kamfanin Media Trust, mai buga jaridar AMINIYA ke bukin cika shekaru biyu da fara wannan jarida mai matukar farin jini, mu ma a wannan shafi na Kimiyya da Fasaha, bayan taya AMINIYA murnar kaiwa wannan lokaci, na farin cikin sheda wa masu karatu cewa a cikin mako mai zuwa, shafin Kimiyya da Fasaha zai cika shakaru biyu cur! Ga wadanda suka fara bibiyan wannan shafi daga lokacin da ya fara bayyana zuwa yanzu, watakil suna iya tuna kasidar farko da ta fara bayyana a wannan shafi, mai taken Fasahar Intanet a Saukake (1). Hakan ya faro ne cikin watan Okotobar shekarar 2006. A yau, cikin yardan Allah, sai ga mu gab da Oktoba ta shekarar 2008. Shekara kwana, in ji Bahaushe! Wannan tasa muka ga dacewar zama na musamman, kamar yadda muka yi a lokutan baya, don yin waiwaye; abin da Malam Bahaushe ke kira adon tafiya.
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.