Waiwaye Kan Darussan Baya (3)
Idan mai karatu bai mance ba, makonni kusan ashirin da suka wuce ne muka zauna don yin Waiwaye Adon Tafiya kashi na biyu. A yau kuma cikin yardar Allah gashi mun sake dawowa don maimaita irin wannan zama. Kamar yadda muka sha fada, amfanin wannan zamfa shi ne don yin tsokaci, tare da kallon baya, da halin da ake ciki, da kuma inda za a dosa nan gaba. A yau ma kamar sauran lokutan baya, mun kasa wannan kasida zuwa kashi hudu da kuma kammalawa. A bangaren farko za mu yi bita kan kasidun baya. Sai kuma bayani kan mahangar da wadannan kasidu suka ginu a kai. Daga nan sai muyi tsokaci kan wasikun masu karatu. Ba wai nassin wasikun za mu kawo ba, don kusan duk na amsa su ko. Sai abu na karshe, wato bayani kan inda muka dosa a zango na gaba. Sai a biyo mu!