Baban Sadik

Idan baka samu kasida ko maudu’in da kake nema ba…

A LURA:  Dukkan kasidun dake wannan shafi suna da tsayi, domin kasidu ne da suka kunshi bincike na ilimi, ba wai labaru bane.  Don haka, idan tsayinsu ya gundureka,  kayi hakuri.  Dabi’ar mahallin ne.

Sakonni (2017)
Baban Sadik

Sakonnin Masu Karatu (2017) (20)

A yau ga mu dauke da wasu daga cikin sakonnin da na samu ta wayar salula da kuma Imel.  Ina kara kira ga masu aiko sakonni cewa a rika hadawa da cikakken suna da kuma adireshi; ko kuwa a ta wayar salula aka aiko.  Nan gaba duk sakon da aka aiko babu cikakken suna ko adireshin mai aikowa, ba za a buga ba.  Da fatan za a kiyaye.

Sauran bayanai »
Kere-Kere
Baban Sadik

Yawaitar Motoci Masu Makamashin Lantarki a Duniya: Ina Muka Dosa? (2)

Kasar Sin ta ba da sanarwar daina amfani da motoci masu amfani da makamashin man fetur da dizil a kasarta zuwa shekarar 2040.  A makon jiya mun fara yin nazari kan sakon dake dunkule cikin wannan sanarwa nata, da kasashen da suka yi wanann kuduri kanfinta, da sakamakon hakan ga kudaden shigarmu a Najeriya, sannan a karshe muji bayani kan motoci masu amfani da makamashin lantarki da yanayinsu.  Ga kashi na biyu cikin wannan nazari namu nan.  A sha karatu lafiya.

Sauran bayanai »