Baban Sadik

Idan baka samu kasida ko maudu’in da kake nema ba…

A LURA:  Dukkan kasidun dake wannan shafi suna da tsayi, domin kasidu ne da suka kunshi bincike na ilimi, ba wai labaru bane.  Don haka, idan tsayinsu ya gundureka,  kayi hakuri.  Dabi’ar mahallin ne.

Fasaha
Baban Sadik

Nau’ukan Fasahar Sadarwa a Intanet (4)

A makon da ya gabata idan masu karatu basu mance ba, mun kawo bayanai kan tsarin da masu tashoshin talabijin suke bi ne wajen yada shirye-shiryensu, da kuma nau’ukan shirye-shiryen da suke da su a shafukan Intanet.  Wannan mako, kamar yadda muka yi alkawari, zamu dubi hanyar sadarwa ta jarida ce da mujallu da suka mamaye giza-gizan sadarwa ta Intanet, kamar wutar daji.  Har wa yau, za mu dubi irin tsarin da suke bi wajen yada labarai da kasidu da makaloli.  Idan shafuka basu mana halinsu ba, zamu kawo wasu daga cikin jaridun da ke da shafukan yanar gizo a Intanet.

Sauran bayanai »
Fasaha
Baban Sadik

Nau’ukan Fasahar Sadarwa a Intanet (3)

A makon da ya gabata mun fara kawo bayanai kan tsarin da ke tattare da yada labarai da wakoki a gidajen yanar sadarwa na tashoshin rediyo da ake dasu a giza-gizan sadarwa ta duniya.  Mun kuma nuna irin hanyoyin da su ke bi wajen taskance labaran musamman ga tashoshin FM masu sayar da wakoki ko kuma yada taskantattun shirye-shiryen su.  Har wa yau, ba mu karkare wancan mako ba sai da muka tabbatar da cewa mun kawo bayanai kan dukkan makale-makalen da suka dace mai son sauraron labarai da shirye-shiryen tashoshin rediyo ta Intanet ke bukata kafin yayi hakan.  A yau kuma cikin yardan Ubangiji za mu kama hanya in da za mu ji irin tsarin da masu tashoshin Talabijin ke bi a nasu harkan.

Sauran bayanai »
Fasaha
Baban Sadik

Nau’ukan Fasahar Sadarwa a Intanet (2)

 Mun fara kawo mukaddima a makon da ya gabata kan nau’ukan fasahar sadarwa da ke giza-gizan sadarwa na Intanet.  Inda muka fara da irin dalilan da suka haddasa yaduwar nau’ukan wadannan hanyoyin sadarwa a Intanet, duk da cewa suna da nasu muhallin da su ke ta taka rawa shekaru kusan hamsin da suka gabata.  A yau muka ce za mu ci gaba da koro bayanai kan ire-iren wadannan nau’ukan hanyoyin sadarwa, da tsarin da suke gudanuwa a kai da kuma yadda mai karatu zai iya amfana da wadannan hanyoyi ba tare da ya mallaki nau’urorin da ake sauraro ko saduwa da su ba.  Bisimillah, wai an hada Malamai kokawa:

Sauran bayanai »
Fasaha
Baban Sadik

Nau’ukan Fasahar Sadarwa a Intanet (1)

Akwai nau’ukan hanyoyin sadarwa dake cikin Intanet, kamar su talabijin da rediyo da jaridu. Daga wannan mako za mu dubi wadannan hanyoyin sadarwa, da tsarinsu a Intanet da kuma irin fasahar da suke dauke dashi.

Sauran bayanai »
Fasaha
Baban Sadik

Mudawwana – “WebLog” ko “Blog” – (2)

 Idan mai karatu bai mance ba, a makon da ya gabata mun kawo bayanai ne kan Mudawwanar Intanet, wato Web Log, a turance, da tarihinta da kuma yadda ake mallakar mudawwana ga duk mai son yada nasa ra’yin don wasu su karanta a giza-gizan sadarwa ta duniya.  Na san da dama cikin masu karatu sun fara himma wajen gina nasu mudawwanar, sakamakon sakonnin da nai ta samu ta Imel da wayar salula da kuma bugowa ma da wasu suka yi, don neman Karin bayani.  Haka ake so daman.  Wannan na daga cikin abin da nai ta jaddada mana cikin kasidar Waiwaye Adon Tafiya, wato kwatanta abin da aka koya ko karanta, a aikace.  Da haka harkan ilimi ya ci gaba a duniya gaba daya.  Don haka duk wanda ya fara ginawa, to ya natsu ya karasa.  Wanda bai fara ba, ya fara.  Wanda kuma ya gama ginawa, ya aiko mana da adireshin don mu ziyarce shi, mu ga abin da yake tallata ma duniya a tsarin tunaninsa.  A yau za muci gaba da bayanai kan Mudawwana har wa yau, sai dai za mudan maimaita wasu gabobin bayanan da muka yi, kafin mu zarce, don na fahimci wasu na samun matsala.

Sauran bayanai »
Fasaha
Baban Sadik

Manhajar Matambayi Ba-Ya-Bata (Search Engine)

Manhajar “Matambayi Ba Ya Bata” ita ce ke taimakawa wajen zakulo bayanai a ko ina suke adane a gidajen yanar sadarwa na duniya. A yau zamu dubi wannan manhaja ne, da amfaninta, da kuma misalai na wasu kamfanoni guda uku.

Sauran bayanai »
Fasaha
Baban Sadik

Mashakatar Lilo a Intanet (Cyber Cafe)

A makon da ya gabata, mun yi zama ne don nazari kan kasidun baya da tasirinsu wajen taimaka ma mai karatu kara saninsa da fahimtarsa kan wannan hanyar fasahar sadarwa da abin da ya shafe ta.  A haka za mu ci gaba da kawo bayanai, muna zama lokaci-lokaci, don yin waiwaye, abin da wani bawan Allah mai suna Malam Bahaushe ya ce “adon tafiya” ne.  A wannan mako, za mu yi bayani ne kan Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake, wato Cyber Café, a turance.  A yanzu za mu dukufa!

Sauran bayanai »
Fasaha
Baban Sadik

Lilo da Tsallake-Tsallake a Intanet (Web Browsing)

A ƙasidar da ta gabata, mun gabatar da taƙaitaccen bayani kan Gina Gidan Yanar Sadarwa (Web Design), da abubuwan da mai ginin ke buƙata kafin ya fara aikinsa.  A wannan makon kuma ga mu ɗauke da bayanai kan yadda mai ziyara zai yi Lilo da Tsallake-tsallake a irin waɗannan gidajen yanar sadarwa don neman bayanai ko ganin duk abin da yake son gani a cikinsu.

Sauran bayanai »