Alakar Intanet da Harkokin Rayuwa (3)

Makonni biyu da suka gabata mun kawo bayanai kan alakar da ke tsakanin Intanet da harkokin yau da kullum. Inda muka sanar da mai karatu abubuwa da dama na abin da ya shafi harkokin rayuwa da yadda ake gabatar dasu a duniyar Intanet. Duk da yake mun yi alkawarin kawo samfurin yadda ake hakan a aikace daga wasu daga cikin gidajen yanan sadarwan wasu hukumomi ko kamfanoni ko bankuna, a wannan mako, zan so su mu yi tsokaci ne kan fa’i’dojin da ke tattare da yin hakan a yau. In ya so sai mu kawo misalai a aikace a mako mai zuwa. Wannan zai taimaka ma mai karatu sanin dalilan da suka sa galibin kamfanoni da hukumomin gwamnati ke ta kai gwauro suna kai mari wajen gina gidajen yanan sadarwa da kuma shigar da harkokin da ke tsakaninsu da abokan huldansu zuwa can, duk da dan Karen tsadan da yin hakan ke tattare dashi.

Karin Bayani...