Saƙonnin Masu Karatu (2024) (5)

Alaƙar Binance P2P Da Farashin Dala

An buga wannan maƙala ne a jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 10 ga watan Mayu, 2024.

34

Alaƙar Binance da Farashin Dala (Ci gaba)

Shahararru cikin nau’ukan kuɗaɗen zamani da ake hada-hadarsu a wannan cibiya dai sun haɗa da: “Bitcoin”, da “Etha”, da “XRP”, da “SOLANA”  da sauransu.  Bayan rajista, kana iya zuba kuɗi a taskarka (Wallet), sannan ka sayi nau’in kuɗin da kake son saya.  Bayan wasu lokuta idan farashin kuɗin ya tashi, sai ka sayar don samun riba.  Ba wannan kaɗai ba, cibiyar Binance na da na’ukan fasahohin aiwatar da kasuwancin Kiripto kala-kala.  Hatta bashi kana iya ci don sayan kiripto.  Idan ka sayar sai ka biya.  Wannan shi suke kira: “Margin Trading”.  Bayan shi ma, kana iya cin bashin nau’in kuɗin kiripto don riƙewa idan farashinsa ya tashi ka sayar ka samu riba. Wannan shi ake kira: “Crypto Lending”.  Sai dai wannan nau’i na bashi ko aron kuɗi, yana ɗauke ne da kuɗin ruwa, wato riba (Interest).  Wanda kuma a musulunci haramun ne.

Har wa yau, wannan cibiya ta Binance na ɗauke da hanyoyin ajiyan kuɗaɗe daban-daban.  Kana iya amfani da taskarka na banki,  ko katin ATM dinka, kai tsaye don zuba kuɗi a lalitarka ta Binance.  Ko kuma, kayi amfani da taskar ajiyarka ta dala ko fam na Ingila (Domiciliary Account); duk cibiyar na ɗauke da waɗannan damammaki.  Haka idan ka tashi sayayya.  Bayan haka, cibiyar Binance na ɗauke da kasuwanni iri biyu ne.  Kasuwar farko ita ce wacce za ka iya zuwa ka sayi haja kai tsaye, a cire kuɗin daga taskarka.  Wannan kasuwa ita ake kira “Spot Market”.  Sai kasuwa ta biyu wacce kasuwar lalura ce.  A wannan kasuwar, idan ka gama ƙulla ciniki da abokin cinikinka, ta bayan fage ake biyan kuɗi, kafin ya miƙa maka hajar da ka saya.  Wannan kasuwar ita ake kira: “Peer-to-Peer”, ko “P2P Market”.

Tsarin P2P

- Adv -

Tsarin P2P (Peer-to-Peer), wanda kasuwa ce dake bai wa masu cinikayya daman ciniki da juna kai tsaye amma biyan kuɗi sai ta bayan fage, an samar da ita ne saboda lalura, kamar yadda na bayyana a sama.  A kasuwar farko, wato “Spot Market”, nau’in kuɗi kawai za ka gani, sai ka matsa, sannan ka rubuta nawa kake buƙata, idan saya za ka yi.  Kana gama rubutawa nan take za ka ga adadin kuɗin da za ka biya.  Idan ka amince, sai ka biya da katinka kai tsaye, wanda tuni ake sa ran ka ɗora a kan cibiyar sadda kazo rajista.  Daga nan za a cire kuɗin, sannan a loda maka kuɗaɗen da ka saya a shafinka, ba ɓata lokaci.

Amma a kasuwar P2P ba haka lamarin yake ba.  Ga dai yadda ake cinikayya nan a taƙaice.  Idan kana da wasu kuɗaɗe da kake son sayarwa, akwai inda za ka je ka tsara tallan kuɗaɗen.  Wannan shi ake kira: “Binance Ad”.  Wajen tsarawa, za ka rubuta guda nawa kake son sayarwa (ba guda nawa ka mallaka ba), sannan a wani farashi kake son sayarwa?  Misali, idan kana da USDT ne, wanda nau’in kuɗi ne dake wakiltar dalar Amurka.  Mu ƙaddara kana da guda 1,000 da kake son sayarwa.  Sai ka rubuta adadinsu, sannan ka rubuta a farashin da kake son sayar da kowane ɗaya.  Bayan haka, za ka rubuta iya  adadin lokacin da idan an samu mai saya, za ka karɓi tayinsa, idan ya biya kuɗin kuma zai sanar dakai duk ta hanyar manhajar ko shafin.  Muddin lokacin ya wuce mai saye bai aika kuɗi ba, nan take za a warware tayin.  Haka idan mai hajar yaga dama, yana iya warware tayin a ɓangarensa.  Wannan shi ake kira: “Transaction cancellation”.

Amma idan aka yi sa’a ya biya kuɗin ta taskar ajiyarka, akwai inda zai sanar dakai.  Kai kuma sai ka bincika taskar ajiyarka ta banki, idan kuɗin sun shiga, sai ka sake masa adadin kuɗaɗen da ya saya. Ba lalai bane ya sayi dukkan adadin kuɗin da kake tallatawa.  Kuma a babin tsaro, idan aka samu wanda ya karɓi tayinka, nan take za a kulle kuɗaɗen da ka tallata; ba za ka iya cirewa ko ragewa ko ƙara su ba.  Ana hakan ne don tabbatar da tsaro ga mai saye.  Kada sai mutum ya gama biyanka kuɗi kuma ka waske.  A taƙaice dai, wannan shi ne bayani kan tsarin P2P a cibiyar Binance.  Ba ma Binance kaɗai ba, kusan duk cibiyar dake da wannan tsari, haka abin yake gudanuwa.  Ana samun bambanci ne kawai wajen hanyoyin warware husuma tsakanin mai saye da mai sayarwa idan rikice ya ɓarke.  Me saye na iƙirarin ya biya kuɗi, mai sayarwa kuma na cewa bai ga kuɗi ba.  Haka na faruwa sosai.

To me yasa aka ƙirƙiri tsarin P2P?  An samar da wannan hanyar cinikayya ne don sauƙaƙe wa waɗanda ba sa iya amfani da katin banki (ATM) ko tsarin banki wajen biyan kuɗaɗe da karɓan kuɗin dake da alaƙa da kasuwancin kiripto a ƙasashensu.  Ba kowace ƙasa bace ake iya gudanar da wannan nau’in kasuwanci na kiripto.  Kamar yadda ba a kowace ƙasa ake iya amfani da cibiyar Binance ba.

A ƙasashe irin su Malaysia misali, ba ka iya amfani da wannan cibiya ta Binance.  A Najeriya ma tun shekarar 2017 babban banki (CBN) ya haramta wa bankuna aiwatar da hada-hadan kuɗaɗen zamani, saboda haɗarin dake tattare dasu.  Shi yasa idan ɗan Najeriya ne kai, ba ka iya saya ko sayen komai a cibiyar Binance da katinka na ATM; an kulle.  Amma idan ta tsarin P2P ne, kana iya loda lambar taskar ajiyarka na banki a shafinka, a duk sadda ka ɗora talla, duk wanda ya karɓi tayinka idan ya tashi biyan kuɗi zai ga suna da lambobin taskar ajiyarka.  Ta nan zai biya kai tsaye.  Ka ga an waske wancan hani kenan da hukuma tayi.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.