Saƙonnin Masu Karatu (2024) (3)

Alaƙar Blockchain da Kirifto Ne Kaɗai?

An buga wannan maƙala ne a jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 26 ga watan Afrailu, 2024.

39

Alaƙar Blockchain da Kirifto ne Kaɗai?

Cin Moriyar fasahar Blockchain bai taƙaitu ga amfani da ita wajen hada-hadar kiripto kaɗai ba.  A a, ko kaɗan.  Wannan ɗaya ne daga cikin hanyoyin cin moriyar fasahar.  Daga cikin waɗannan hanyoyi akwai tsarin amfani da ita a bankuna don taskance bayanan jama’a, da tsarin aikawa da karɓan kuɗaɗe cikin sauƙi.  Ƙarƙashin wannan fanni har wa yau, ana iya amfani da fasahar Blockchain wajen hada-hadar kasuwancin hannun jari, wato: “Stock market transactions.”  Sannan kamfanonin hada-hadar kuɗi ta hanyar fasahar sadarwa ma na iya gina manhajoji a sanan wannan tsari, don bai wa abokan hulɗarsu damar aiwatar da kasuwanci cikin sauƙi.  Wannan tsari duk yana ƙarƙashin cin moriyar fasahar Blockchain ne a ɓangaren hada-hadar kuɗaɗe.  Ire-iren waɗannan manhajoji su ake kira: “Decentralized Finance Apps”, ko “DeFi Apps”.

Haka nan cikin hanyoyin cin moriyar wannan fasaha akwai amfani da ita wajen ƙirƙirar hajojin fasaha da ake iya taskancewa da sayar dasu ta kafofin sadarwa na zamani. Waɗannan su ake kira: “Non-Fungible Tokens” ko “NFTs” a harshen fasahar sadarwa na zamani.  Hajoji ne da suka ƙunshi zane, ko taswira, ko wasu kayayyaki na fasaha waɗanda babu wanda ya taɓa ƙirƙirar irinsu a duniya, kuma babu wanda zai mallake su sai ta hannun wanda ya samar dasu.  Ana amfani da fasahar Blockchain don taskance su da hana ‘yan dandatsa isa gare su cikin sauƙi.

Hanya mafi girma da inganci na cin moriyar fasahar Blockchain ita ce ta amfani da manhajar Smart Contract.  Wannan manhaja ce dai hanya ce da ake ƙirƙira a kan fasahar Blockchain, mai ɗauke da ƙa’idojin yarjejeniyar kasuwanci, waɗanda da zarar an gina su cikin manhajar, kai tsaye za su riƙa gudanuwa; ba a bukatar lauya wajen sake rubuta su, sannan ba a bukatar bibiyar abokin mu’amalar kasuwanci.  Ta wannan tsari ne kamfanoni a duniya suka fara samar da wasu sababbin hajoji na kasuwanci wadanda kai tsaye za ka iya hawa shafinsu don isa garesu da ƙulla alaƙa da su.

Har way au, ana amfani da manhajar Smart Contract wajen rajistar inshora, da taskance bayanan marasa lafiya a asibitoci, da yin rajistar lasisin motoci, da taskance bayanan kadarorin jama’a, da taskance bayanan da suka shafi kayayyakin abinci da wasu kamfanoni ke yin odarsu tun daga gona har zuwa inda za a sarrafa su.  Bayan haka, a wasu ƙasashe tuni an fara amfani da manhajar wajen taskance bayanan fulotai da ke ƙarƙashin hukumomi.

A ƙarshe dai, ƙasar Amurka ta fara amfani da wannan tsari na Smart Contract wajen zaɓe.  Ma’ana, hukumar zaɓe na iya amfani da wannan tsari wajen bai wa kowane ɗan ƙasa da ya isa jefa ƙuri’a, damar yin hakan, ta hanyar bashi ƙwandala guda, misali, ko “token” kamar yadda ake kiransu. Sannan ayi rajistan dukkan ‘yan takaran da ake son zaɓansu ta hanyar bai wa kowannensu adireshi ko lambar taska.  A ranar zaɓe, sai ka hau shafin jefa ƙuri’a kawai, ka ɗauki wannan ƙwandala da hukumar zaɓe ta baka, ka aika wa wanda kake son zaɓa.  Ka jefa masa ƙuri’a kenan.

- Adv -

Bayan an gama jefa ƙuri’a, tsarin tantance bayanai dake ɗauke a fasahar Blockchain ɗin ne zai tarkato dukkan ƙwandalolin da aka jefa wa ‘yan takara, sannan ya ƙididdige su.  Abin da aka jefa shi kawai za a gani.  Sannan ba wanda zai iya jefa ƙuri’a sau biyu.  Ko jefa wa mutane biyu a matsayin ɗaya, ko kuma yunƙurin canza wanda ya zaɓa. Galibin matsalolin da muke fuskanta wajen jefa ƙuri’a za su kau.

A takaice dai, wannan kaɗan ne cikin abin da za a iya yi da wannan fasaha ta Blockchain, kuma kamar yadda bayani ya gabata, tana cikin jerin fasahohin da ake sa ran za su jagoranci kawo sauyi a wannan saha ta giza-gizan sadarwa na duniya.

Da fatan ka gamsu da ɗan bayanin da ya samu kan wannan fasaha ta Blockchain.

Assalamu alaikum, barka da warhaka Malam Baban Sadiƙ.  Haƙiƙa muna jin daɗin wannan shafi naka. Muna kuma godiya ga hukumar Aminiya dake ɗaukan nauyin wannan ɗawainiya da kake yi wajen bincike don faɗakarwa.  Ni ƙarin bayani ne kawai nake so kan, wasu hanyoyi ne kamfanonin wayar salula a Najeriya ke bi wajen sadar da kwastomominsu da siginar Intanet?  Domin na karanta maƙalar da rubutu kwanakin baya kan tsinkewar wayoyin kebul dake karkashin teku, amma har yanzu na kasa fahimtar lamarin.  Ka huta lafiya.  Ni ne ɗalibinka kuma takwaranka: Abdullahi Adamu Iyal, Bauchi, Bauchi State, Najeriya. Iyaladam222@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai takwarana. Na ji daɗi ƙwarai da jin cewa ɗan ƙoƙarin da nake yi wajen faɗakawar na bayar da fa’ida sosai.  Allah ƙara amfanar damu baki ɗaya, amin.

Na fahimci sarƙaƙiyar da ka samu kanka a ciki na rashin fahimtar wannan tsari da hanyar da kamfanonin waya ke bi wajen haɗa ka da siginar Intanet.  Tabbas kowa ma haka abin yake a gare shi muddin ba ganin abin kayi a aikace ba.  Haka lamarin ilimi yake; muddin ba fanninka bane, dole a wasu lokuta a samu wahala wajen fahimtar yadda wasu abubuwan suke, musamman ma abin da ya shafi harkar sadarwa.  Yana da sarƙaƙiya sosai.  Amma kuma ba abu bane da ake iya kasa fahimta ɗari bisa ɗari.

Kamfanonin wayar salula na amfani da hanyoyi biyu ne mahimmai wajen sada ka siginar Intanet, a matsayinka na mai amfani da katin wayarsu, a kadadar sadarwarsu (Network Coverage Area).  Shekaru kusan 15 da suka gabata na gabatar da doguwar maƙala kan tsarin sadarwar wayar salula, a doguwar maƙalarmu mai tare: “Bayani Kan Wayar Salula”, wacce nake sa ran ita ce maƙala mafi tsayi da a jerin maƙalolin da aka taɓa bugawa a wannan shafi mai albarka.  Wancan bayani ya shafi tsarin sadarwar siginar rediyo ne, wayo “Radio Signal Communication”.  Amma abin da ya shafi tsarin siginar Intanet, ban yi dogon bayani akai ba sai cikin ‘yan makonnin da suka gabata kamar yadda ka gani.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.