Saƙonnin Masu Karatu (2024) (1)

An buga wannan maƙala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 12 ga watan Afrailu, 2024.

58

Kamar yadda muka saba lokaci zuwa lokaci, daga wannan mako zuwa makonni uku dake tafe, za mu amsa wasu daga cikin tambayoyinku ne.  Idan an tashi aiko saƙonni a rika kyautata rubutu, sannan a sanya adireshi don tantance wanda ke aiko saƙo.

———————–

Assalamu alaikum Baban Sadik.  Barka da warhaka. Da fatan ka sha ruwa lafiya.  Na karanta bayananka kan fasahar AI da abubuwan da za ta iya yi, musamman ma wacce ke aikin samar da bayanai kai tsaye, wato Generative AI.  Amma a tsari gamamme, ta wasu hanyoyi ne fasahar AI ke da nasaba da fannin ƙere-ƙere.  Fatan za ka sha ruwa lafiya. Allah karɓi ibadojinmu baki ɗaya, amin. Ni ne naka, Ɗahiru Ɗan Baiwa Mai Gwanjo, Legas, a Najeriya – dahirubaiwa30@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ɗahiru.  Fatan kana lafiya kaima. Allah karɓi ayyukanmu baki ɗaya, amin.  Dangane da tambayarka, lallai akwai nasaba mai  ƙarfi tsakanin fasahar AI da fannin ƙere-ƙere; ya Allah na motoci ne, ko na wayar salula ko ma wane ɓangare ne.

Da farko dai, zai dace mu san cewa, fannin AI tsari ne da ya ƙunshi tsofa wa na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani, ɗabi’u da halayyar ɗan adam, don sawwaƙe tsarin ma’amala dasu.  Shi yasa masana a harshen Hausa ke fassara Artificial Intelligence da “Ƙirƙirarriyar Basira”.  Muna iya ɗaukan ƙerarriyar na’ura ko mota ko jirgi a matsayin gangar jikin ɗan adam misali.  Sannan mu ɗauki basira da ƙwaƙwalwar ɗan adam a matsayin abubuwan da aka loda wa na’urar ko motar don ba ta damar gudanar da ayyukanta iya yadda ake so.

Dangane da haka, akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin kamfanonin sadarwa dake samar da manhajoji da fasahohin AI, da kuma kamfanonin ƙere-ƙere a ɓangarori daban-daban.  Kamfanonin ƙera wayoyin salula na alaƙa da kamfanonin gina manhajar fasahar AI, don loda wa wayoyin salula da basu damar ma’amala da mai wayar, ko sarrafa bayanan da wayar ke ɗauke dasu kai tsaye, da sawwaƙe wa mai wayar hanyoyin amfani da ita ko da mahallinsa.  Kusan galibin wayoyin salula na zamani a yau suna ɗauke da wannan fasaha ta AI, kuma hakan ya yiwu ne sanadiyyar alaƙar kasuwanci dake tsakanin kamfanonin da masu samar da manhajojin fasahar AI.

A ɓangaren motoci na zamani kuma, musamman motoci marasa matuƙi, suna amfani ne da fasahar AI wajen tantance mahallin da suke, da sarrafa bayanan mahallin, da kuma iya gudanar da aikinsu cikin sauƙi.  A ɗaya ɓangaren kuma, kamfanonin ƙera na’ura mai fasaha (Smart Devices) na amfani da manhajojin fasahar AI ne kai tsaye, don samar da waɗannan manhajoji. Haka ma kamfanonin ƙera na’urar mutum-mutumi da ake amfani da su a masana’antu da kamfanonin ƙera-ƙeren na’urori masu nauyi – irin su jirgin sama, da manyan motoci na zamani da saurnasu – duk suna da alaƙa ta kai tsaye da masu ginawa da lura da manhajojin fasahar AI a duniya.

- Adv -

A taƙaice dai, duk wata na’ura dake ɗauke da fasahar AI, an samar da ita ne ta hanyar yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kamfanin da ya ƙera na’urar da kamfanonin sadarwa na zamani da suke gina waɗannan manhajoji kuma suke lura dasu.  A duniyar yau, da wahala ka samu kamfani ɗaya a fannin ƙere-ƙere, kai, kowane fanni ma, wanda ke samar da komai da komai daga kayayyakin ƙere-ƙere da yake amfani dasu.  Dole ne ya raba ƙafa.  Abubuwan da suke buƙatar ƙwarewa, yakan samar dasu ta hanyar waɗanda suka ƙware a fannin.  Wannan shi ake kira: “Outsourcing”.  Wannan tsari na rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa ne wajen ƙere-ƙere da hada-hadar kasuwanci.  Duk abin da ba ka buƙatarsa, ba za a ajiye shi ba.

Da fatan ka gamsu da wannan taƙaitaccen bayani.  Na gode.

Assalamu alaikum, barka dai Malam Baban Sadiƙ.  Fatan kana lafiya. Me ake nufi da fasahar Blockchain?  Sannan, alaƙarta ta taƙaitu da fasahar kirifto ne kaɗai?  Na gode sosai, Allah saka da alheri ya kuma albarkaci zuri’a baki ɗaya, amin. – Masoyinka: Auwalu Ibrahim, Gabasawa, gabasawa2001@yahoo.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Auwalu. Ina godiya matuƙa da addu’o’inku.  Allah saka da alheri.

Da farko dai, fasahar Blockchain tsari ne da ya ƙunshi gamammen rumbun adana bayanai a Intanet wanda ke cike da kariya da aminci, kuma duk bayanan da aka adana a cikinsa babu mai iya canza shi.  Bayan haka, wannan tsari yana cin gashin kansa ne; ma’ana babu wata hukuma ko gwamnatin wata ƙasa ko wani kamfani da yake kula dashi ko ƙayyade tsarin ma’amala a kansa.  A kan wannan tsari na Fasahar Blockchain ne ake aiwatar da cinikayyar hada-hadar kuɗi na Bitcoin, da Etha da sauran nau’ukan kuɗaɗen zamani da ake amfani dasu ta hanyar Intanet kaɗai.

Da wannan ne wasu ma ke ganin kamar Bitcoin shi ne haƙiƙanin fasahar Blockchain.  Wannan ba haka yake ba.

Fasahar Blockchain maɗauki ne, ko ince mahalli ne mai ɗauke da kariya kuma mai cin gashin kansa, inda duk masu neman kariya da aminci na bayanai, da gamewar tsari ke zuwa don samun natsuwa.  Asalin waɗanda suka samar da tunanin wannan fasaha dai su ne Mista Stuart Haber da kuma Scott W. Storuatta, manyan masana fannin lissafi a ɗaya daga cikin manyan jami’o’in Amurka.  A cikin shekarar 1991 ne suka fitar da wata maƙalar bincike wadda a ciki suka yi bayanin hanyar samar da wani tsarin samarwa da taskance bayanai wanda zai dogara ga tsarin tantancewa ta hanyar tairihi ko rubutaccen lokacin da aka kirkira ko taskance bayanan.  Wannan, shi ake kira: “Time-stamp” a harshen fasahar sadarwa na zamani.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.