Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (15)

Fina-Finai da Littafai Kan Satar Zati

Saboda shahara da dadewar wannan nau’i na ta’addanci a duniya, akwai wasu fina-finai da aka yi su don fadakar da jama’a kan hakan.  Bayan fim ma, akwai littafi na musamman, wanda shi ne ya gabata kafin bayyanar tsarin fim ma a duniya.  Wannan littafi mai suna:  The Prisoner of Zender, an rubuta shi ne a shekarar 1894, shekaru 124 kenan yanzu da rubuta wannan littafi.  A cikin littafin an ba da labarin yadda wasu abokan hamayyar wani sarki na gargajiya da ake gab da nadawa bayan rasuwar wanda ya gada ne, inda masu hamayyar suka sa masa sinadarin maye a cikin abinci a jajibirin nadinsa.  Kuma a al’adar wannan al’umma, duk Sarkin da ya kasa halartar ranar nadinshi, to, sarautar ta wuce shi kenan.

‘Yan uwansa da suka gan shi a buge, irin buguwar da ko gari ya waye bazai iya wartsakewa ba, sai suka san lallai makirci ne wannan.  Don haka suka je suka yi hayan wani dan kasar Ingila dake bakonta garin, wanda ta duk inda ka kalli sarki bugagge, ba yadda wannan Ba’ingile ya rage shi.  Kamarsu daya, kamar an tsaga kara.  Shi suka dauko a boye, aka masa nadi a matsayin shi ne Sarkin, kuma shi aka rantsar.  Da haka suka sha.

Fim na farko kuma shi ne The Stolen Identity, wanda aka shirya shi a shekarar 1953.  A cikin wannan fim dai wata baiwar Allah ce ta sace wa wani bawan Allah zatinsa.  Inda take ta amfani da sunan da bayanansa a duk inda taje.  Har ta kai ga an dauka ita ce hakikanin mai sunan.  Sai Fim na karshe mai suna: Idnetity Thief.  An shirya wannan Fim ne a kasar Austria dake nahiyar Turai ta yanzu, a shekarar 2013.  Kuma shi ma, kamar sauran, maudu’insa shi ne kan satar zati da munin hakan cikin al’umma, musamman na wannan zamani.

DandatsaFasahaIntanet
Comments (0)
Add Comment