Sakonnin Masu Karatu (2015) (2)

Assalamu alaikum, a gaskiya na ji daɗin wannan labari na jirgin taitanic, Ubangiji Allah ya kara fasaha.  Ameen.  Rabo  –  binmuhammad723@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam Rabo, ina godiya da addu’arka.  Allah saka da alheri, amin.  Na gode.


Assalamu Alaikum, da fatan kana lafiya kuma komai ma lafiya lau, ameen.  Allah ya taimaki Baban Sadiq ya kara masa fasaha da mu ma baki daya, ameen.   Don Allah ina son a bani bayani akan “Windows 11 PC” da kuma hotunanta (Screen Shorts) nata idan kana da su. Na gode.  – Prince of Lovers Abdoolmaleek – 07033328759, 08068042758

Wa alaikumus salam Malam Abdulmalik, barka ka dai.  Ina godiya da addu’o’inku baki daya.  Dangane da tambayarka, ba na tunanin akwai wata babbar manhaja mai suna: “Windows 11,” tukunna dai.  Sai dai “Windows 10,” wacce ina kyautata zaton ita ce kake nufi.  In haka ne, na san tuni ka karanta hirar da BBC Hausa suka yi dani a ranar da aka kaddamar da babbar manhajar, kuma an buga hirar a wannan shafi mai albarka.

Idan baka samu karantawa ba, kana iya turo mini adireshinka na Imel sai in tura maka rubutacciyar hirar gaba dayanta; shafuka 7 ne.  Ko kuma kaje shafina dake Dandalin Facebook (www.facebook.com/babansadik), ka gangara bangaren hotuna, za ka ci karo hotunan wannan sabuwar babbar manhaja, tare da hotunanka, kamar yadda ka bukata.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu Alaikum.  Sunana Bashir Sani Suleiman, na turo maka sako ta lambar MTN dinka kan cewa ina so don Allah ka bani cikakken tarihin rayuwarka.  Har na turo maka email dina, amma banga komai ba.  Shi ne nace bari in turo maka ta nan ko Allah zai sa in dace.  –  Bashir Sani Suleiman daga Pambegua, Kaduna State.  Nagode.  –  bashirsanisuleiman@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Bashir sannu da kokari.  Tabbas na samu sakonka amma saboda shagulgular yau da kullum ban samu amsa maka bukatarka ba.  A gafarce ni.  Na kuma ga sakonka na Imel, kamar yadda kake gani yanzu, cikin dacewar Ubangiji na samu tura maka dai a halin yanzu.  Sai ka duba akwatinka na Imel don daukan sakon.  Sai dai wani hanzari ba gudu ba, bayanin da na tura maka ba cikakke bane, domin na ga kace kana bukatar “cikakken tarihina” ne, wanda kuma a gaskiya bazai samu ba yanzu, sai in kana nufin har zuwa ranar da nake wannan rubutu ne.  Sai dai kayi hakuri da abin da ya samu, wanda kuma shi ne takaitaccen tarihin da na buga a wannan shafi shekaru 5 da suka gabata, sanadiyyar bukata irin wannan daga masu karatu.  Na gode.


Allah Ya saka da alheri.  Tabbas muna gamsuwa da binciken da kuke yi mana.  Allah ya kara fahimta, amin. Wannan binciken da kuke yi yana nuna mana girman ikon Ubangiji ne. Don haka muji tsoron Allah.  –  Muhsin Sabiu –  muhsinsabiu@gmail.com

Wannan zance haka yake Malam Muhsin.  Duk sadda mai bincike ya kutsa cikin duniyar ilimi zai ga abubuwan mamaki matuka dangane da halittar Ubangiji da yadda yake sarrafa duniyar baki daya.  Mafi girman rabo da mai bincike zai samu shi ne karin tsoron Allah cikin abin da ya gani na girman Ubangiji musamman kan abin da ya shafi halittar duniya da sauransu.  Allah sa mu dace baki daya, amin.


Amincin Allah ya tabbata a gareka Baban Sadiq. Yaya ayyuka, da gida da sauransu? Da fatan kana lafiya, uhum Baban Sadiq, daman ina neman wata yar alfarma ce a gare ka. Alfarmar kuwa ita ce, a taimaka mini da kasidar nan na ta Dabarun Bincike A Internet.  –  Abubakar Sadeeq.  mrsadeeq44@gmail.com

Malam Abubakar barka ka dai.  Kana iya duba akwatin Imel dinka, tuni na aika maka da kasidar gaba dayanta.  Allah sa a amfana baki daya, amin.


Assalamu Alaikum, marashin iyakan gaisuwa gareka shigafarta, kuma takwarana. Don Allah ina da bukata ka aiko min da dukkan kasidunka masamman wadanda kayi akan ilmin Kwamfuta.  –  bnlmustapha@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam Mustapha.  Wannan bukata ce mai girma.  In Allah ya yarda zan samu lokaci don tantance wadanda zan iya turo maka.  Kasidun suna da yawa, sun fi 300.  Ka ga idan nace duka zan turo maka zan dauki lokaci.  Don Allah a min uzuri, da zarar an gama bukukuwan sallah za ka ga abin da ya sawwaka.  Da fatan za a gafarceni kan gazawata.  Na gode.


Salaamun alaikum. Baban Sadiq barka da warhaka. Ban san wane irin taimako za ka iya yi min ba, na yi duk yadda zan yi na sauke babbar manhajar “Windows 10” amma abin ya ci tura, ko wata kila don Windows din da nake amfani da ita ba na kamfani bane? Don Allah me ye abin yi?  Na yi kakarin yin downloading ta hanyar updating windows ne.  Sannan idan na sayi 3GB zai iya sauke min manhajar?  –  Nura Gwanda

Wa alaikumus salam Malam Nura, da fatan kana lafiya.  Ban san wace irin matsala kake fuskanta ba.  In har babbar manhajar Windows da kake amfani da ita ba gangariya bace, jabu ce, to zai yi wahala ka iya saukar da ita ta hanyar Windows Update.  Mu kaddara babbar manhajar taka orijina ce, amma a sadda Updates din suka bayyana ka ga na Windows 10?  In eh, ta yiwu siginar Intanet dinka ne bai da karfi, ko kuma ba ka da isasshen data. Domin mizanin manhajar ya kai 2.8GB. Ka ga kuwa idan ba ka da isasshen Data zai yi wahala ka iya saukar da ita.

Bayan haka, mizanin data 3GB yayi kadan gaskiya, domin ta yiwu akwai wasu updates din da kwamfutarka za ta dauko tare da Windows 10 (idan ka dade baka yi ba kenan).  Amma kana iya gwadawa.  Sai dai matsalar ita ce, idan har aka samu akwai wasu Updates, wanda kimar mizaninsu yafi 3GB, muddin su aka fara saukarwa kafin manhajar Windows 10 din, da zarar data ya kare kafin ta gama, komai zai koma sabo, ma’ana sai ka sake sabon zubi.

FasahaKwamfutaWayar Salula
Comments (0)
Add Comment