Kimiyyar Sararin Samaniya a Sawwake (3)

Al-Kur’ani  mai girma a cike yake da tsarin nazari kan sammai. Ga ayoyi nan birjik masu kiran dan Adam zuwa yin dubi da izna da tunani cikin halittun sararin samaniya don ganin irin kawa da kuma kimtsin da Allah ya yi musu.  Bucaille (1976:135-151) ya gano ayoyi sama da hamsin cikin Kur’ani masu magana kan halittun da ke sararin samaniya da duniyar ma gaba daya.  A karshe yake cewa:

“A nan ma, ba karamin abin sha’awa bane, musamman idan aka gwama bayanan da Kur’ani ya yi da bayanan Kimiyyar Zamani a bangare daya, da kuma bayanan  da ko kadan ba a hada su da tunanin mutumin da yayi rayuwa shekaru dubu daya da dari hudu da suka gabata, a daya bangaren.”

Ba ma Ilimin Sararin samaniya kadai ba, hatta Ilimin Duniya a dunkule (Cosmology) ma musulunci ya sanshi. Shi ne ilmin da ya kumshi halittar duniya gaba daya da dukkan abin da ke cikinta.  Shi ne dadadden nau’in kimiyyar da manyan littattafan sama guda uku suka karantar: Attaura, da Linjila da kuma Kur’ani.

Halittar sammai da kasa gaba dayansu da abin da suke dauke da shi, duk sun samu ne cikin ikon Allah.  Kur’ani ya yi bayani kan taurari, da rana, da wata, da irin tsarin da  duniya ke gudanuwa a ciki, mai ban al’ajabi.  A zamanin yau, fannin Ilmin Duniya a Dunkule (Cosmology) ya zama wani bangare ne cikin fannin Ilmin Kimiyya, kuma shi ne ke lura da tarihin abubuwan da suka faru tun shekaru aru-aru da suka gabata.  Wannan kalma wadda a turance ake kira “Cosmology”, ta samo asali ne daga kalmomi guda biyu cikin harshen Girka; ‘Kosmos’ wadda ke nufin ‘tsari’, da ‘kintsuwa’, da ‘duniya,’ da kuma Kalmar ‘Logos’ mai nufin ‘bincike’ ko ‘tattaunawa’ (kan wani abu).  Don haka, a takaice dai abin da kalmar Cosmology ke nufi shi ne Ilmin duniya gaba dayanta.

A warware kuma, wannan fanni na bayani ne kan buruji ko masaukan taurari, da ranar karshe, da abin da zai faru ga dukkan taurari, da wannan duniyar tamu, da wata, da ma yadda duniyar gaba daya za ta kasance a karshe.  Dukkan wadannan halittu Allah ne ya halicce su, kuma gaba dayansu duk za su gushe a karshe; kuma gare shi za a tayar da dukkan rayuka don ya yi musu hisabi.  Sannan bayan haka, an umarci dukkan musulmi da su yi dubi zuwa ga sama, su zurfafa tunani kan tsarin halittarta don su dada fahimtarsu dangane da girman Ubangiji Mahalicci.  Akwai ayoyin Kur’ani masu yawa da suka zo kan haka.

Kur’ani mai girma ya sifata tsarin halittar duniya baki daya, kuma wajibi ne a ilmantar da kananan yara don su fahimci tsarin halittar Ubangiji mai ban mamaki da ke gewaye da su. A lokacin da mutum ke karami ba zai fahimci wadannan ayoyi ba, saboda an saukar da Kur’ani ne cikin harshen Larabci. Amma abu ne mai sauki idan aka saurari tafsirin malamai.  Kamar sauran kananan yara, na samu daman karanta Kur’ani tun ina dan karami, kuma na fahimci mahangar musulunci dangane da halittar duniya gaba dayanta.  A takaice ma dai, na iya cewa wannan na daga cikin abin da yayi tasiri matuka wajen sanya mini sha’awar fannin Ilmin Sararin Samaniya.  Na dada samun karfin gwiwa a lokacin da malamina mai suna Malam Zakariya ya sanar da ni cewa, “Idan kana son sanin Allah, to ka kalli sama, za ka ga abubuwan mamaki da al’ajabi.”  Kuma wannan shi ne abin da Allah ya fada cikin Kur’ani.  A takaice na iya cewa addinin Musulunci ne ya kara mini kwarin gwiwa kan wannan fanni.

Gudunmawar Malaman Musulunci

Kur’ani mai girma ya tabbatar cikin ayoyi masu dinbin yawa cewa, halittar duniya baki daya aya ce da ke nuna samuwar Ubangiji.  Bayan haka, ni’ima ce cikin ni’imomin da Ubangiji ya bai wa bayinsa.  Kur’ani ya tabbatar da cewa duniya gaba dayanta an halicce ta ne da gaskiya, ba don wargi ko wasa ba.  Don haka, koyon Ilmin Sararin Samaniya, wanda yana daya daga cikin nau’in ilmin kimiyya, ba abu bane na wasa; hanya ce ta koyon tarbiyya da imani.  In kuwa haka ne, wajibi ne duk mai koyonsa ya kyautata manufa da niyyarsa.

Sai bayan na girma ne na ci karo da littattafan tarihin musulunci masu dauke da bayanai kan gudunmawar da Malaman musulunci suka bayar wajen ci gaban fannin Ilmin Sararin Samaniya.  Wannan ci gaba kuwa ya samo asali ne ta hanyar Malaman musulunci da suka yi rayuwa a kasashen Larabawa, da kuma wadanda suka rayu a daular Andalus tun cikin karni na takwas miladiyya, a birnin Kodoba (Townson, 1973:12).  Duk da haka, tarihi ya nuna cewa Ilmin Sararin Samaniya ya samo asali ne daga Jazirar Larabawa.

Malaman musulunci masana Kimiyya sun kwankwadi ilmin fannin Sararin Samaniya ne daga zamanin da ya biyo zuwan musulunci; musamman daga birnin Mesopotamia, da daular Fasha, da Indiya, da kuma daular Sin, wadanda suka kware cikin wannan fanni na Ilmin Sararin Samaniya.  Wadannan dauloli da suka yi zamani kafin zuwan musulunci sun yi amfani ne da Ilmin Taurari da kuma jabun ilmin sararin samaniya.  Har wa yau, Malaman Musulunci sun fara amfani ne da kayayyakin binciken sararin samaniya na da, wadanda aka gada daga daulolin Indiya da Sin.  Aristatalis ne ya fara yin sharhi kan rubuce-rubucen babban malamin falsafalan nan na daular Girka – wanda ya yi da’awar cewa dukkan taurari suna tsaye ne daura da wannan duniya, kuma ba su motsawa.  Bayan shi kuma sai Fakhr Al-Din al-Razi, wanda yayi zamani a karni na goma sha uku.  Al-Razi ya tabbatar da cewa babu dalili cikin wannan zance na Aristatalis da ke cewa taurari ba su motsawa (Al-Faruqi, 1986:332).

AstronomyDr. Adnan AbdulhamidKimiyyaSararin SamaniyaWhy Astronomy
Comments (2)
Add Comment
  • USMAN MUAZU

    ALLAH YASAKAMA DA ALHERI,DON ALLAH INASON SANIN GIDAJEN YANAR GIZO DA AKE NEMAN ILLIMI

  • Usman Abubakar Musa

    Menene gaskiyar magana akan taurari,shin suna tafiya ne ko aa,Yaya girmansu yake da wannan duniyartamu, shin duniyartamu atsaye take ko Tana tafiya,Rana fa Tana tafiya ne ko aa?