Kimiyya da Fasaha a Kasashen Musulmi (6)

Sauyi a Kasashen Musulmi

Muna Buqatar Sauyi

A baya mun bayyana raunin hujjojin masu dogara kacokan akan raunin da Musulmai suka yi a fagen ci gaban kimiyya da fasaha na alaqantuwa ne da wani sashi na malamai dake kore haxuwa da dacewar kimiyya da addini. A’a, alal haqiqa abin da ya haifarwa da qasashen Musulmai cibaya a fagen ilimi ya dogara ne a kan yadda tsarin gudanar da mulkinsu, wato administrative ke tafiya a kan tsohon tsarin da duniya ba ta tafiya da shi yanzu. Sai kuma yadda tsarin gudanar da tafiyar da qasarsu ke dogara a kan wasu tsiraru masu faxa a ji ba wai waxanda al’umma suka zava ba. Wannan ne tsarin da Turawan mulkin mallaka suka xora akasarin qasashen Musulmai na OIC da har yanzu suke girbarsa; kuma har yanzu sun gaza samar da wani tsarin da ya fi shi ko makwafinsa. Hakan na faruwa ne sanadiyyar rashin samar da kyakkyawan tsarin gudanar da mulki da zai kawo canji ga wannan tarnaqin, ya kuma yaqi cin hanci da rashawa, da kuma samar da tsarin ilimi da koyarwa mai nagarta da qarko da suka dace da qarni na 21, da kuma samar da cibiyoyi na ilimi da jami’o’i da za su yi gogayya da takwarorinsu na Turai da qasashen Yammacin Duniya.

Sai kuma a qarshe uwa-uba gyara da saita tunanin ‘yan qasa akan yadda za su zamanto masu son cicciva qasashen nasu gaba a vangaren binciken kimiyya da fasaha da kuma kawo wa al’ummar tasu ci gaba. Amma dai za mu ce Alhamdulillah yanzu ganin yadda ake ta samun sauye-sauye a tarayyar qasashen Musulman cikin sauri a ko da yaushe.

Tsakanin Musulmai da waxanda ba Musulmai ba kowa ya san lokacin da Musulmai ke kan qololuwar ganiyarsu a fagen ci gaban kimiyya da fasaha.  Haka kuma kowa ya kwana da sanin auratayya mai qarfi da aka samu tsakanin addinin Musulunci da kuma kimiyya da fasaha a wancan lokutan. Sani da koyar da hakan ba qaramin gagarumin gudunmowa zai bayar ba wajen ci gaban kimiyya da fasaha a qasashen Musulmai a yau. Hakan bai ma tsaya iya nan ba, domin kuwa zai buxe wata hanya ko wasu hanyoyi da a nan gaba Musulmai za su farga su gane amfani da fa’idar da qishirwar ilimi da qwaqwa ta hanyar yin nazarce-nazarce da bincike a kan kimiyya da fasaha da sauran vangarori na ilimi zai haifar mu su ko kuma ga duniya baki xaya, kamar dai yadda suka yi a shekaru 1000 da suka shuxe lokacin da ludayansu ke kan dawo a duniyar ilimi.

Babbar hanya ta farko ta cimma hakan ita ce ta zuba kuxi da bayar da tallafi na gaske a wannan harkar. Domin kuwa abu ne da yake a bayyane tamkar rana cewa ware gwaggwavan kaso daga kasafin qasa ga vangaren binciken kimiyya da fasaha da sauran ilimomi na haifar da xa mai ido ga ci gaban qasa a fannin kimiyya da fasaha. Abun farin cikin shi ne yadda a yau da yawa daga gwamnatocin qasashen Musulman ke zuba kuxaxe masu kauri a vangaren binciken kimiyya da fasahar duk dai domin su samar da cibiyoyi na binciken kimiyya da fasaha ‘yan aji na farko, wato, World-Class Research Institutions, da suyi kankankan da na sauran qasashen da suka ci gaba a wannan vangaren.  Za mu iya ganin misalin hakan ganin yadda qasashe da yawa daga yankin Larabawa da ake kira da Gulf States kullum ke aikin gina sababbin jami’o’i na zamani da ma’aikatansu ke zuwa daga qasashen Yammacin Turai domin aikin samar da jami’o’in da kuma malaman da za su koyar a cikin su.

Amma fa shawo kan matsalar bai tsaya kaxai ba ne ga narka da zuba maqudan kuxaxe a harkar. A’a, abubuwan da su ne sinadarai waxanda kuma dole sai sun samu sannan za a samu ci gaban kimiyya da fasahar da ake buqata sune damar iko ga shugabanni da jagorori na al’ummar qasashen Musulmai na kawo sauyi ga tsarin shugabancinsu, da kuma tabbatar da sakakken ‘yanci na tunani da nazarce-nazarce (wanda bai sava wa shari’a ba) ba tare da wani tazgaro ko tarnaqi ba ga su masanan dake a qasashen Musulman.  Alal misali, Nader Fergany, wanda shi ne ya jagoranci rahoton Majalisar Xinkin Duniya a kan Ci gaban Xan Adam A Qasashen Larabawa mai suna: United Nations’ 2002 Arab Human Development Report, ya jaddada cewa abubuwan da dole sai sun tabbata a qasashen Larabawa sannan za su kai ga gaci a fagen ci gaban kimiyya da fasaha a duniya sune: 1) sabunta cibiyoyin ilimin kimiyya da fasaha da kuma jami’o’I, 2) sai kuma a samu girmama fahimta da ra’ayoyi mabambatta ko da kuwa sun ci karo da wani ra’ayi karvavve a al’adance, 3) sai kuma tabbatar da kowa da kowa a qasa ya samu ingantaccen ilimi, 4) sai kuma sauyawa da matsar da al’umma daga inda suke zuwa al’ummomi da babu abin da ke gabansu illa ci gaban ilimi da bunqasa shi. Abu na qarshe shi ne, qasashen Larabawan (Musulmai) su tabbatar da sun samu kyakkyawar fahimtar ci a gaba a zamanance, a wannan duniyar ta yau mai xaude da ci gaba a fannin wayewar ilimi. (Mujallar Nature 444, shafi 33).

FasahaKere-kereKimiyyaMusulunci
Comments (0)
Add Comment