Hanyoyin da Kafafen Sada Zumunta Ke Samun Kudaden Shiga (5)

Hajojin Kamfanin Twitter

Kamfanin Twitter na da manyan hajoji guda biyu, wadanda ta hanyarsu ne yake samun kudaden shigarsa.  A tare da cewa ba rasa wasu hajojin wadanda ke samar masa da kudaden shiga, sai dai wadannan guda biyun su ne mafiya girma kuma da su yake dogaro wajen tafiyar da kamfanin ma gaba daya.  A wannan mako in Allah Yaso za mu dubi wadannan manyan hajoji da hanyar da ake amfani dasu wajen samar da kudaden shiga ga kamfanin.

Tallace-Tallace

Hanya ta farko ita ce ta hanyar karban tallace-tallace daga kamfanonin kasuwanci da hukumomin gwamnatocin kasashe, da kuma wasu shahararrun mutane don tallata musu hajojinsu da zatinsu, ko yi musu kamfen idan ‘yan siyasa ne.  Wannan hanya ta kunshi yin rajista ne da Dandalin ko jami’anta dake kasar da kake, a matsayinka na mai son ba kamfanin talla.  A kasashe irin na Afirka misali, kamfanin Twitter na da jami’ai dake karban tallace-tallace a madadinsa, ko kuma kaje shafin kai tsaye don yin rajista da mika tallarka.  Hanyar da kamfanin Twitter ke bi wajen dora wadannan tallace-tallace dai sun kasu kashi hudu.

Hanyar farko ta kunshi tallata sako ne na musamman.  Misali, idan kana da wani sako na musamman da kake son a tallaka maka shi, kana iya biyan kudi, sai a tallata shi.  Wannan shi ake kira: “Single Tweet Ads”.  Abin da suke bukata shi ne, sakon da kake son a tallata maka shi, da nau’in mutane ko jama’an da kake son sakon ya riska – kamar kasa ko nahiyar da suke zaune – da adadin kwanaki ko watannin da kake son a tallata shi.  Ana amfani da wannan nau’in talla ne wajen aikawa da wani sako na musamman, ga wasu mutane na musamman, a wata nahiya ko kasa ko bigiren duniya na musamman, cikin wani lokaci na musamman.

Nau’in talla na biyu kuma ya kunshi tallata shafin wani kamfani ne, ko wani mutum na musamman, da duk sakonnin dake kan shafin.  Wannan shi ake kira: “Twitter Account Ads”, kuma manufar hakan shi ne don bijirar da shafin ga wadanda ake son su gani, don su bibiye (Follow) shi saboda manufar kasuwanci ko siyasa ko wanin wannan.  Galibi idan ka hau shafinka na Twitter kaga an bijiro maka da wasu shafuka (Accounts), a samansu an rubuta: “Who to Follow”, to, wadannan shafukan duk tallata maka su ake yi, idan ka bi kowanne daga cikinsu, kamfanin Twitter zai samu kudin shiga daga kamfani ko mutumin da kabi shafinsa.

Nau’in talla na uku ku shi ne tallata wani maudu’i ko al’amari da ake son ya shahara sanadiyyar wani abu da yake faruwa a wani bangaren duniya misali.  Ko kuma wata kungiya na son fadakar da mutane kan wani abu da ke cikin manufofinta da take son jama’a su fadaka dashi don bata goyon baya a kansa.  Wannan nau’in talla shi ake kira: “Twitter Trends Ads”.  Idan ka hau shafinka na Twitter kaga an bijiro maka da wasu kalmomi dake dauke da sunaye wasu mutane ko hajoji ko kasa ko jumlar zance dake dauke da wani al’amari, a sama kaga an rubuta: “Trending”, to, duk kalma ko jumlar da ka latsa daga cikin wadannan kalmomi ko bayanai da aka bijiro maka dasu, akwai wani kaso na kudin shiga da kamfanin Twitter ke samu daga kamfani ko mutumin da ya bashi alhalin tallata wannan kalma ko al’amari.  Wannan ya sha bamban da “Hashtag”.

Sai nau’in talla na hudu kuma na karshe, wanda ya kunshi dora talla ta hanyar hoton bidiyo da mutane ke dorawa, ko wanda mai talla zai dora mai dauke da sakon da yake son a tallata masa.  Wannan shi ake kira: “In-Stream Video Ads”.  A takaice dai, nau’in talla ne dake dauke kan bidiyo da ake dorawa a wannan dandali na Twitter.

A shekarar 2020 da ta gabata, kamfanin Twitter ya samu dalar Amurka biliyan 3.2 ($3.2 bil) daga wadannan hanyoyin tallace-tallace guda hudu, wato kwatankwacin naira tiriliyon 1.6 (N1.60 tr) kenan a Nairan Najeriya.  Wannan shi ne kashi 86 cikin 100 na kason kudin shiga da kamfanin ya samu a shekarar.  Tirkashi!

Tsarin “Twitter Data Licensing”

Hanya ta biyu da kamfanin Twitter ke bi wajen samun kudaden shiga bayan karban wadancan nau’ukan tallace-tallace guda hudu dai ita ce ta hanyar sayar da lasisin amfani da bayanan da kamfanin ke tarawa na mutanen dake mu’amala a dandalin, ga kamfanonin kasuwanci da masu bukata.  Wadannan bayanai sun hada da yawan masu rajista da dandalin a kowace kasa a duniya, da adadin jinsinsu, da adadin launukansu, da dandanonsu na rayuwa, da nahiyoyinsu, da na’urorin da suke amfani dasu wajen hawa dandalin, da lokutan da jama’a suka fi hawa dandalin, da dai sauran bayanai.  Kamfanin Twitter kan karbi kudade wajen kamfanoni, don basu damar shiga taskar bayanansa da amfanuwa da wadannan bayanai kai tsaye, don manufofi na kasuwanci.  Wannan tsari na kasuwanci shi suke kira: “Twitter Date Licensing”.

A shekarar 2020 da ta gabata, kamfanin Twitter ya samu dalar Amurka miliyan 509 ($509.00 Mil), kwatankwacin naira biliyan 255.5 (N255.40 bil) a Nairan Najeriya kenan.  Wannan shi ne kashi 14 cikin 100 na kudaden shiga da kamfanin ya samu a shekarar.

FacebookGoogleIntanetTwitter
Comments (0)
Add Comment